Wata babbar kotun Abuja ta bada belin tsohon babban sakataren hukumar inshorar lafiya ta Najeriya (NHIA), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar tuhume-tuhumen aikata almundahana.
Matakin bada tallafi ga iyalin Fulanin da ‘yan fashin daji suka raba da shanunsu a Najeriya na daya daga hanyoyin dawo da zaman lafiya a wasu jihohin Arewacin kasar
A wani mataki na nuna goyon baya, masoyansa sun taru a kofar shiga ginin majalisar, sun rera wakoki da jinjina ga dan majalisar mai wakiltar mazabar Agege a majalisar
‘Yan sanda sun tabbatar da sace dalibai mata daga jami’ar tarayya ta Joseph Tarka da ke Makurdi, wacce a baya ake kira da jami’ar aikin gona ta tarayya.
Masanin kimiyyar kididdiga Farfesa Sadik Umar ya nuna mamakin yadda taron ya tashi ba tare da jan hankalin shugaban kan halin da kasa ke ciki na kuncin tattalin arziki ba.
Yarjejeniyar ta bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da bayar da “tallafin kudi domin samar da wata Ukraine mai zaman lafiya da wadata ta fuskar tattalin arziki.”
Sanarwar ta kara da cewa sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 27 ga watan Fabrairun 2025.
A zaman kotun na karshe a Litinin din data gabata, Emefiele, ta hannaun babban lauyansa, Olalekan Ojo, ya nemi Mai Shari’a Oshodi ya janye daga sauraron karar.
Mai Shari’a Osiagor ya ba da umarnin adana wadanda ake zargin a kurkukun Najeriya tare da dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Yunin 2025.
Majalisar Dattawan Najeriya ta jaddada kudurinta na cewa za ta yi la'akkari da shawarwarin jama'a masu ma'ana wajen amincewa da gyaran kudirin dokokin inganta haraji a kasar.
Duk da bayanan da mahukunta ke yi a kan samun sassaucin hare-haren ‘yan bindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya, wasu al’ummomi kuwa har yanzu suna kokawa ne a kan hare-haren ‘yan bindigar a yankunansu.
Domin Kari
No media source currently available