Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Emefiele Ya Yi Rashin Nasara A Yunkurinsa Na Dakatar Da Shari’a


Tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele
Tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele

A zaman kotun na karshe a Litinin din data gabata, Emefiele, ta hannaun babban lauyansa, Olalekan Ojo, ya nemi Mai Shari’a Oshodi ya janye daga sauraron karar.

Kotun hukunta laifuffukan musamman da ke Legas ta ki dakatar da sauraron zarge-zargen almundahanar da ake yiwa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

A hukuncin da ya zartar a yau Laraba, Mai Shari’a Rahman Oshodi ya yi watsi da bukatar ya tsame kansa daga sauraron karar, inda yace babu hujja kan zargin da ake yi masa na nuna karkata da son zuciya.

Da take kafa hujja da jerin hukumomin shari’a, kotun tace karkata ko nuna son zuciya a shari’a ba zai wadata ba wajen tabbatar da rashin cancantar alkali ko neman ya tsame hannunsa daga shari’a, inda ta kara da cewa wajibi ne ta kasance ta shafi alkalin a kashin kansa ko kuma wani tunani na shari’a.

Daga bisani alkalin ya zartar da cewar bukatar neman ya tsame hannunsa daga shari’ar ba ta da hujja kuma nan take ya yi watsi da ita.

A zaman kotun na karshe a Litinin din da ta gabata, Emefiele, ta hannaun babban lauyansa, Olalekan Ojo, ya nemi Mai Shari’a Oshodi ya janye daga sauraron karar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG