Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta gurfanar da karin ‘yan China 16 a gaban babbar kotun tarayyar Najeriya, dake Legas.
An gurfanar da mutanen ne a gaban Mai Shari’a Daniel Osiagor a jiya Talata kan zargin aikta ta’addanci ta hanyar na’ura da zambar intanet da nufin yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa.
Mutanen na cikin mambobi 792 na gungun wadanda ake zargi da zambar zuba jarin kudin kirifto da ta kulla soyayya da aka kama a ranar 10 ga watan Disamban 2024, a jihar Legas, a wani samame da jami’an hukumar EFCC suka kai.
An gurfanar da mutanen ne a bisa tuhume-tuhume daban-daban, da ke da nasaba da laifuffukan na’ura da ta’addanci ta na’ura da malakar takardun da ke kunshe da zamba cikin amince da kuma satar bayanan mutane.
Dukkanin mutanen sun ki amsa laifin aikata tuhume-tuhumen da ake yi musu sa’ilin da aka karanto musu su, sakamakon hakan lauyan masu kara, Nnaemeka Omewa, ya bukaci kotun ta tsayar da ranar fara sauraron shari’ar tare da adana wadanda ake tuhuma a kurkukun Najeriya.
Sakamakon hakan, Mai Shari’a Osiagor ya ba da umarnin adana wadanda ake zargin a kurkukun Najeriya tare da dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Yunin 2025.
Dandalin Mu Tattauna