Najeriya ta haura matsayi biyar a cikin shekarar bara ta 2024, inda ta tashi daga matsayi na 145 zuwa 140 a cikin kasashe 180 na duniya bayan da ta samu maki daya a cikin sabuwar kididdigar.
Karin wani bangare na karin kaso 50 cikin 100 na harajin kiran waya da sayen data, da hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince da shi saboda halin da kasuwa ke ciki a halin yanzu.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Muhammad Idris, ne ya sanar da umarnin yayin ganawa da manema labarai a Abuja a yau Talata.
Babban daraktan hukumar samar da lantarki a karkara (REA), Abba Aliyu, yace da zarar Shugaba Bola Tinubu ya zartar da kasafin kudin zuwa doka, hukumarsa za ta fara aikin samar da lantarki a makarantun gwamnatin.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta bayyana cewar ta samu nasarori a yakin da take yi shan miyagun kwayoyi, musamman da hadin gwiwar jihohi da kananan hukumomi.
A watan Yunin 2021 aka dawo da Kanu zuwa Najeriya kuma tun lokacin yake tsare tare da fuskantar shari'a a kan zargin ta'addanci.
Tun a bara asibitin ke fama da daukewar wutar lantarki sakamakon basussukan da kamfanin rarraba hasken lantarki na Ibadan (IBEDC) ke bin sa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Cross River, Liyel Imoke da Sanata Aminu Tambuwal wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Sokoto.
A shirye hukumar take ta yi hadin gwiwa da ‘yan majalisa da sauran masu ruwa da tsaki a kan batun, inda Adeyeye ta koka da karancin ma’aikata a hukumar.
Za’a tattauna da masu ruwa da tsaki yayin taron kwamitin ilimi na kasar da zai gudana a watan Oktoban bana kafin yanke shawara ta karshe game da tayin.
Ga dukkan alamu, duk da kokarin da sojojin Najeriya ke yi wajen yakar 'yan bindiga, har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Domin Kari
No media source currently available