Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zargin Almundahana: Kotu Ta Ba Da Belin Farfesa Usman Yusuf


Farfesa Usman Yusuf
Farfesa Usman Yusuf

Wata babbar kotun Abuja ta bada belin tsohon babban sakataren hukumar inshorar lafiya ta Najeriya (NHIA), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar tuhume-tuhumen aikata almundahana.

A yau Alhamis Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu ta ba da umarnin sakin Farfesa Yusuf daga kurkukun Kuje, bayan cika ka’idojin bada belin.

Hukumar EFCC, mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ce ta gurfanar da Farfesa Yusuf a bisa wasu tuhume-tuhume 5 masu nasaba da zargin almabazzaranci da baiwa kansa damar da bata dace ba, a matsayinsa na shugaban nhis a 2016, ta hanyar amincewa da sayen motoci akan Naira milyan 49, 197, 750 sabanin Naira milyan 30, 000, 000 da aka kasafta kashewa.

EFCC ta kuma yi zargin cewar Farfesa Yusuf ya samu wata dama ta kashin kai a wani kamfani mai suna “Lubekh Nigeria Limited” ta hannun wani dan danuwansa, Khalifa Hassan Yusuf, inda ya bashi kwangilar yada labarai da hulda da jama’a ta Naira milyan 17, da dubu 500.

Wanda ake tuhumar yaki amsa laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG