Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Yarjejeniyar Ma’adinai Da Za A Kulla Tsakanin Amurka Da Ukraine


Shugaba Volodymyr Zelensky (hagu) da Shugaban Amurka Donald Trump (Dama)
Shugaba Volodymyr Zelensky (hagu) da Shugaban Amurka Donald Trump (Dama)

Yarjejeniyar ta bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da bayar da “tallafin kudi domin samar da wata Ukraine mai zaman lafiya da wadata ta fuskar tattalin arziki.”

Ukraine da Amurka za su rattaba hannu kan yarjejeniyar ma’adanai mai tarihi, mataki mai muhimmanci wajen karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Duk da haka, masana tsaro sun shaida wa VOA cewa har yanzu akwai damuwa game da tasirin yarjejeniyar gaba daya.

Majalisar Ministocin Ukraine ta amince da yarjejeniyar a ranar Laraba, kuma Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, zai kai ziyara Fadar White House a ranar Juma’a domin sanya hannu kan yarjejeniyar.

Yarjejeniyar ta hada da tanade-tanade na mallaka da gudanar da asusun sake gina Ukraine bayan yaki, wanda Ukraine za ta kebe kashi 50 cikin 100 na kudaden shigar da za ta samu daga ma’adanan kasar.

Yarjejeniyar ta bayyana cewa Amurka za ta ci gaba da bayar da “tallafin kudi domin bunkasa wata Ukraine mai zaman lafiya da wadata ta fuskar tattalin arziki.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG