An samu durkushewar layin lantarkin sau daya ne tak a sabuwar shekarar da muke ciki bayan da ya durkushe fiye da sau 10 a 2024, abin da ya jefa sassan Najeriya da dama cikin duhu na sa’o’i masu yawa.
Shelkwatar tsaron kasar tace al’amarin ya faru ne yayin aikin kakkabe ‘yan ta’adda a wata babbar tungarsu da ake kira da Kusurwar Timbuktu.
Ana tuhumarsa ne da laifi guda na kisan kai wanda hukuncin sa kisa ne, wanda ya saba da sashe na 221 kundin “penal code”, na hukunta manyan laifuffuka a arewacin Najeriya.
Sanarwar mai sanya da sa hannun wani babban jami'in shige da fice, A. A. Aridegbe, ta alakanta kungiyar da fataucin mutane da tattara yara da rarraba su a ciki da wajen Najeriya.
Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta ce za ta fadada mizanin arzikin kasa wato GDP ta hanyar sanya boyaiyun sassa kamar tabar wiwi, miyagun kwayoyi, yanar gizo da sauran su.
Mayakan Boko Haram da na ISIS Shiyyar Afurka Ta Yamma (ISWAP), da suka fi gudanar da harkokinsu a jahar Borno, sun auna jam’an tsaro da farar hula, wanda ta haka su ka hallaka 20 tare da kawar da dubban mutane.
A halin yanzu, akwai bankunan kasuwanci da kananan bankunan bada lamuni 26 da ke bayar da katunan Afrigo a fadin kasar.
A hukuncin daya zartar, Mai Shari’a Omotosho, ya kuma haramta kungiyoyin irinta da ke gudanar da harkokinsu a Najeriya, musamman yankunan arewa maso yamma da arewa maso tsakiyar kasar.
IBB yayi hiraraki da kafafen yada labaran cikin gida da na kasashen waje tun bayan saukar shi daga kujerar mulkin Najeriya, yayi kokarin kaucewa batutuwa masu sarkakiya da suka faru a lokacin da yake Mulki.
Ya taba zama mataimakin shugaban jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) kuma an zabe shi Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu a shekarar 2015 a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Makyankyasar jariran na nan a rukunin gidaje dake yankin Ushafa na birnin tarayyar Najeriya.
Domin Kari
No media source currently available