Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ramadan: Sarkin Musulmin Najeriya Ya Bukaci A Fara Duba Watan Azumi Daga Gobe


Majalisar mai alfarma Sarkin Musulmi ta sanar da gobe Juma’a, 28 ga watan Fabrairu, ta zama ranar farko ta duban jinjirin watan Ramadan na shekarar 1446 bayan hijira.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da aka rabawa manema labarai a yau Alhamis a Sokoto, wacce Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin ba da shawarwari a kan harkokin addini a fadar Sarkin Musulmin, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya sanyawa hannu.

A cewar sanarwar, ana umartar al’ummar musulmi su fara duban jinjirin watan a gobe Juma’a tare da kai rahoton ganinsa ga dagaci ko mai unguwa mafi kusa dasu.

Sanarwar ta ƙara da cewa idan ba a ga watan a ranar Juma'a ba, to ranar Lahadi za ta kasance 1 ga watan Ramadan na wannan shekara.

Daga nan kuma za’a aika rahoton ganin watan ga Sarkin Musulmin Sokoto kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar na 3, domin bada sanarwar fara azumin watan Ramadan a hukumance.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG