Yayin da ake tsaka da rikicin shugabancin daya tarwatsa zaman lafiyar da ake da shi a Majalisar Dokokin jihar Legas, hambararren kakakinta, Mudashiru Obasa, ya bayyana a zauren majalisar a yau Alhamis.
Obasa ya samu rakiyar wata tawagar jami’an tsaro masu sanye da kayan sarki kuma dauke da makamai cikin murtakakkiyar fuska sa’ilin daya shiga zauren majalisar wanda rabon da a ganshi a bainar jama’a tun bayan da aka sauke shi daga kan kujerarsa a ranar Litinin, 13 ga watan Janairun 2025.
A wani mataki na nuna goyon baya, masoyansa sun taru a kofar shiga ginin majalisar, sun rera wakoki da jinjina ga dan majalisar mai wakiltar mazabar Agege a majalisar mai mambobi 40.
Idan muka yi waiwaye zuwa watan Janairu, an tsige obasa daga kan kujerar shugabancin majalisar dokokin Legas da rinjayen kaso 2 bisa 3 na kuri’un da aka kada bisa zarginsa da rashin da’a da laifuffuka daban-daban.
Nan take aka maye gurbin Obasa da, mataimakiyarsa ta wancan lokaci, Mojisola Meranda, a matsayin sabuwar kakakin majalisar, abinda ya mayar da ita mace ta farko data taba shugabantar Majalisar Dokokin jihar dake shiyar kudu maso yammacin Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna