Ali Pate ya yabawa mahimmanci gudunmowar da gwamnatin amurka ke baiwa najeriya a fannin kiwon lafiya, musamman ma wajen yaki da cutar kanjamau da tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro.
An hange motoci da jami’an tsaron a ciki da wajen harabar ginin Majalisar Dokokin jihar legas din da ke yankin Alausa na birnin kasuwancin.
Mai Shari’a Ekwo ya amince da bukatar ne bayan da lauyan Diezani, Godwin Inyinbor, ya gabatar da ita kuma lauyan FCC, Divine Oguru, bai kalubalanci hakan ba.
Karamar ministan wajen Najeriya Bianca Odumegwu-Ojukwu ce ta bayyana hakan lokacin da jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills ya ziyarceta a gidan Tafawa Balewa, da ke Abuja.
Al’amarin, wanda ya faru bayan kammala zabubbukan kananan hukumomi a asabar din data gabata, ya faru ne sakamakon yunkurin jami’an tsaro na dakile wani harin da ‘yan bindiga suka kitsa kaiwa kan masu kada kuri’a a kauyen Zakka.
Gwamnan Kaduna seneta Uba Sani ya ce “al’umma za su sake zaban APC a duk matakai daga sama har kasa. A can sama shine jagoran mu, shugaba Bola Ahmad Tinubu zai yi tazarce a zaben 2027. A matakin jiha kuma, jam’iyyar zata yi nasara, har da matakan majlisar tarayya da ta jihohi da izinin Allah.”
Majalisar koli ta musulunci a Najeriya karkashin Sultan Muhammad Sa'ad ta dage babban taron mahaddata Al-kur’ani a Abuja zuwa wani lokaci a bayan azumin watan Ramadan.
Nasarar da askarawan yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ta samu ce tayi tasiri wajen yanke shawarar kafa irinta a bangaren lantarkin
Gwamnan na jihar Legas wanda shi ne shugaban kungiyar ya nanata aniyar gwamnonin ta daukar kwararan matakai domin tabbatar da zaman lafiya da daidaito a tsakanin al’ummominsu”.
An tsara cewa Shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya a ranar Litinin, 17 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya ta amince da kasafin Kudin bana mafi girma sabanin yadda aka saba a watan Janairu zuwa Disamban kowacce shekara a baya.
Domin Kari
No media source currently available