Shugaban kwamatin kudi na Majalisar Dattawa, Sanata Sani Musa, ya tabbatar da hakan a wata zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala sauraren ba'asin jama'a kan dokar da a yanzu haka ke gaban Majalisar domin yin mahawara da amincewa da ita.
Ya ce majalisa za ta yi gyaran dokar haraji a daidai wannan lokaci don inganta kudaden shigar gwamnati da bunkasa tattalin arzikin kasa ne ba domin wani sashi ba.
“Majalisa tana wannan gyara ne domin gobe, saboda haka idan mutum yana son shari'a ta zama ta gaskiya dole ne a cire son kai, saboda doka da shari'a duk daya ne,” in ji Sani.
Su ma ana su bangaren kungiyoyi masu zaman kansu da dama ne suka bayyana ra'ayoyinsu a game da dokar gyara haraji ta Najeriya inda suka ba da shawarar cewa a cire harajin VAT, musamman a kan kayan aikin gona.
Kungiyoyin sun ce a babi na 6, sashe na daya, sashe na 143,144,145 da 147 na dokar kula da haraji, ya kamata a canja su zuwa “Ci ko cinyewa'' maimakon ''Kayyadewa da kayayyaki''.
Tsohon Ministan Kudi, Dokta Yarima Ngama, ya ce idan aka duba harajin da ake tarawa da dukiyar da ke Najeriya za a ce ma ba a tara haraji baki daya ma saboda harajin kashi 9.4 cikin 100 na dukiyar da ke Najeriya, saboda haka za a iya cewa ma ba tara komi.
Ngama ya ce idan an duba alkaluma da suke fitowa daga kashen waje za’a ce kashi 6.4 ciki 100, bara waccan kam kashi 5 cikin 100 ne wanda kusan a duniya gaba daya ma Najeriya ce kasar da ta ke komawa baya wajen tara haraji.
Har ila yau, dandalin ya so a bayyana kalmar "derivation" a sarari kuma ba tare da wata shakka ba, yayin da ya kamata a raba shi bisa yarjejeniyar da aka cimma ta hanyar tuntubar jihohi da kananan hukumomi da kuma shawarwarin Hukumar Tattara Kudade da Kasafta su wato Revenue Mobilization and Fiscal Commission a turanci.
Wakilin Kungiyar Tuntuɓa ta Arewa – ACF, Dokta Saidu Dukawa, ya ce dokar kamar yadda gabatarwasu ta kunsa, ba wata aba ba ce ta kyama, saboda mutane da dama suna kokawa kan yadda haraji ya yi yawa yanzu.
Kafin buɗe dandalin sauraren ba'asin jama'a, Majalisar Kasa ta tuntuɓi hukumomin cinikayya da harkokin kudi tare da aiki da shugaban bangaren shari'a wajen gyara dokar.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna