Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilan, Benjamin Kalu, ya ba da sanarwar cewa babu ko guda daga cikin bukatun kirkirar jihohi a Najeriyar da ta dace da bukatun kundin tsarin mulkin da har za’a duba ta.
Mahukunta a Najeriya na ci gaba da nuna damuwa a kan yadda ake samun waiwayowar hare-haren 'yan bindiga a wasu wurare duk da yake cewa jami'ai na kan kokarin kawar da matsalar
Sassan sun hada da unguwar rukunin gidajen ‘yan majalisu ta Apo da Apo Resettlement da Gudu da Apo Mechanic da unguwannin da ke kewaye dasu.
A hukuncin da ya zartar yau Juma’a, Mai Shari’a Yallim Bogoro ya kuma ba da umarnin kwace jarin dala 900, 000 da ake alakantawa da wata ‘yar uwar Emefiele, Anita Joy Omolie, a mataki na dindindin.
Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills Junior ya ce babu wata hujja da za ta sa Amurka ta amince da zargin da ake ma Hukumar Raya Kasashe ta Amurka USAID cewa ita ke tallafa wa Kungiyar Boko Haram
An soke zaben tun gabanin a ayyana wanda ya samu nasara.
A ranar 13 ga watan Febrairun da muke ciki ne, dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya zargi USAID da daukar nauyin kungiyoyin ‘yan ta’adda, ciki harda Boko Haram.
Matsalar rashin tsaro na ci gaba da tayar da hankulan jama'a a Arewacin Najeriya, duk da yake kwanan nan jami'an tsaro na cewa suna samun galaba ga yaki da 'yan ta'adda
Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ce dakarun sojin kasar sun dukufa wajen farautar fitaccen shugaban ‘yan bindigar nan Bello Turji kuma bada jimawa ba zasu gama da shi.
A ci gaba da kokarin samo kudin shiga, hukumomin Najeriya sun yanke shawarar karbar haraji a ATM, a yayin da ake dada korafi kan matsin rayuwa
Domin Kari
No media source currently available