A hirarsa da manema labarai ta wayar tarho, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe, csp Sewuese Anene, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda yace an kaddamar da bincike da kokarin kubutar da wadanda aka sace.
“An sace dalibai mata guda 4 a harabar jami’ar da misalin karfe 8 da rabi na dare, abinda ya haddasa firgici game da amincin daliban kasancewar yankin na makwabtaka da garuruwan da suka yi fama da hare-haren makiyaya.
“An bayyana wasu daga cikin daliban da al’amarin ya rutsa dasu da Emmanuella Oraka, wacce ba komai a jikinta illa zani daurin kirji sai Fola wacce ke sanya da riga ruwan dorawa da Susan mai riga mai launin furanni da kuma Ella me sanye da bakar riga,” a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan.
Dandalin Mu Tattauna