A shirye hukumar take ta yi hadin gwiwa da ‘yan majalisa da sauran masu ruwa da tsaki a kan batun, inda Adeyeye ta koka da karancin ma’aikata a hukumar.
Za’a tattauna da masu ruwa da tsaki yayin taron kwamitin ilimi na kasar da zai gudana a watan Oktoban bana kafin yanke shawara ta karshe game da tayin.
Ga dukkan alamu, duk da kokarin da sojojin Najeriya ke yi wajen yakar 'yan bindiga, har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Yayin da Janhuriyar Nijar ke dada daukar tsauraran matakai kan harkokin shigi da fici, ta na kuma sassauta ma bakin da ke cikin kasar
Shugaba Tinubu ya rushe majalisar gudanarwar jami’ar tare da sauke Farfesa Aisha Sani Maikudi daga kan mukaminta na shugabancin Jami’ar Yakubu Gowon.
Mataimakin Kakakin Majalisar Benjamin Kalu wanda ya jagoranci zaman majalisar na yau Alhamis ne ya karanta wasikar da ta fito daga kwamitin da ke dauke da sunayen jihohin da aka ba da shawarar kirkirar.
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun sace tsohon babban daraktan hukumar kula da matasa ‘yan hidimar kasa a Najeriya (NYSC), Manjo Janar Mahrazu Tsiga (mai ritaya).
Yankin Arewa Maso Tsakiyar Najeriya ya samu hukumar kulawa da matsalolinsa kamar yadda yankunan Naija Delta da Arewa maso Gabas ke da nasu.
A cewar Onanuga, ziyarar shugaban zuwa kasar da ke nahiyar Turai ta kashin kai ce, inda ya kara da cewa Tinubu zai yi ziyarar ne a kan hanyarsa ta zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha
Domin Kari
No media source currently available