Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mata Da Kananan Yara A Zamfara


Taswirar Jihar Zamfara
Taswirar Jihar Zamfara

Duk da bayanan da mahukunta ke yi a kan samun sassaucin hare-haren ‘yan bindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya, wasu al’ummomi kuwa har yanzu suna kokawa ne a kan hare-haren ‘yan bindigar a yankunansu.

Rundunar sojin Najeriya ta ba da tabbacin cewa tana kan fatattakar ‘yan bindigar, inda ta ce ta kashe manya-manyan su da dama musamman a cikin watan nan, kamar yadda babban hafsan sojin kasar Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana a wata ziyara da ya kai jihar Zamfara a kwanan nan, inda ya umurci dakarun sojin da su kawo ma shi shahararren dan bindigar nan Bello Turji a cikin wata daya.

Sai dai al’ummomin yankunan karkara na ci gaba da fuskantar matsin lamba a kan hare-haren ‘yan bindigar kamar yadda wasu mazauna yankin gundumar Kanwa a karamar hukumar Zurmi da Kuryar Madaro a karamar hukumar Kaura Namoda suka bayyana.

Shi kuwa wani da ke gundumar Kuryar Madaro ta karamar hukumar Kaura Namoda, ya ce ‘yan bindigar sun farmakin garin ne a wani yankin da ake Kira Tungar Kosau inda suka kashe mutum 7 tare da raunata wasu.

Ko a daren ranar Talata sai da ‘yan bindigar suka tare hanyar Mayanchi zuwa Anka suka kwashi ‘yan kasuwa da dama da ke kan hanyar dawowa daga kasuwar mako mako ta Talatar Mafara suka kuma shiga garin Anka a Unguwar Mundogara suka dauki wasu mutanen.

Da yake tsokaci a kan lamarin dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ya ce lamarin yana da rikitarwa ganin yadda ake samun sauki kuma sai lamarin ya rikice a wani gefen.

“Mu namu isar da sakon al'umma ne kuma muna Kan yi, abun yayi Kamari Kam, mun samu labarin sai dai muna rokon Allah duk Mai hannu a ciki ki waye shi Allah ya mana maganin shi.” Inji Hon. Aminu.

Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi shi ne mai magana da yawun dakarun tabbatar da tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya wato Operation Fansar Yamma, ya ce tabbas suna samun galaba a kan ‘yan bindigar kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba.

Ya ce “Muna ci gaba da samun galaba a kan su don a wata mun kashe manya manyan ‘yan bindigar da dama, kamar su Na-Faransa, Bokkolo, Kachalla Sani Banmuwa da Sani black da dai sauran su.”

Ga alamu dai akwai bukatar mahukunta su sake lale da bullowa da wasu sabbin matakan samar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin na arewa maso yammacin kasar domin wankin hula na kokarin kai su dare.

Saurari cikakken rahoton Abdulrazaq Bello Kaura:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG