Gwamnatin jihar Neja tare da hadin gwiwar kungiyar Bago Ruga-Ruga sun dauki nauyin tallafawa matan Fulani da nufin rage masu radadin matsin rayuwa.
Duk da cewa ana zargin kabilar Fulani musamman matasa da hannu dumu-dumu a tabka ta’asar yin garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa da satar shanu harma da kisan jama’a babu dalili.
A gefe guda akwai dubban iyalan kabilar Fulanin da suka shiga halin gararamba saboda raba su da dabbobinsu a sakamakon matsalar ‘yan fashin daji.
Matan Fulani guda 100 ne suka samu kashin farko na tallafin Naira dubu dari kowaccensu tare da bude musu wani katafaren dandalin sayar da nono da madara na zamani a tsakiyar kasuwar Minna fadar Gwamnatin jihar Neja.
Hassan Shiroro shugaban kungiyar Bago Ruga-Ruga ya ce ko baya ga wannan tallafi akwai tallafin shanu na musamman ga Fulanin da aka sace ma shanun anan gaba.
Ba da wannan tallafi da sanya cibiyoyin karbar makamai ga Fulanin yafi yin tasiri wajen samar da zaman lafiya a mai maikon yin sulhu da masu rike bindigogin a daji in ji tsohon shugaban miyatti Allah na Najeriya Hardon Paiko da Husaini Yusuf Bisso.
Kwamishinan kula da harkokin makiyaya na jihar Nejan Umar Sanda Rebe ya ce bisa la’akari da yadda matan Fulanin ke dawainiya da iyalai bayan sace shanun mazajensu yasa suka dauki wannan mataki.
Wasu daga cikin matan da suka samu wannan tallafi na dubu 100 sunce zai taiamaka masu wajan bunkasa kasuwancin nono da saida kaji.
Ayanzu dai al’umma na cike da fatar samun saukin wadan nan ‘yan fashin daji masu satar shanun da suka addabi jama’a shekara da shekaru.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:
Dandalin Mu Tattauna