Majalisar Dattawan Najeriya ta jaddada kudurinta na cewa za ta yi la'akkari da shawarwarin jama'a masu ma'ana wajen amincewa da gyaran kudirin dokokin inganta haraji a kasar.
Duk da bayanan da mahukunta ke yi a kan samun sassaucin hare-haren ‘yan bindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya, wasu al’ummomi kuwa har yanzu suna kokawa ne a kan hare-haren ‘yan bindigar a yankunansu.
A jiya Litinin aka ba da rahoton mutuwa Lawal wanda ‘yan sandan Uganda suka ce dan wasan haifaffen Sokoto ya mutu ne bayan daya fado daga benen wani kaafaren kanti.
A sanarwar hadin gwiwar da suka fitar, ‘yan majalisar tarayyar sun yi watsi da dakatarwar, inda suka bayyanata da wacce ta saba doka.
A martanin da ya mayar cikin wata sanarwa, Ribadu yace bai taba tattaunawa da kowa game da yin takara a 2031 ba.
Majalisar wakilan Najeriya ta ce hauhawar shaye-shayen miyagun kwayoyi da cin zarafin da ke faruwa a gidaje babbar barazana ce da ka iya durkusar da Najeriya idan masu ruwa da tsaki ba su hada karfi da karfe ba.
Barayin da ake zargi sun arce bayan da suka hangi dakarun.
A Talatar da ta gabata kungiyar ta tsunduma wani yajin aikin sai baba ta gani sakamakon rashin warware wasu batutuwa tsakaninta da hukumomin jami’ar da suka samo asali tun daga shekarun 2009 da 2017.
A cewar rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, gobarar ta tashi ne bayan da wata katifa dake daure a bayan motar ta taba salansa, abinda ya sabbaba tashin mummunan tashin wuta.
Aiyedatiwa, gwamnan jihar mai ci ya samu kuri’u 366,781 inda ya doke abokin karawarsa na Jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Ajayi Agboola, wanda ya samu kuri’u 117,845.
Domin Kari
No media source currently available