Masaukin Bakin gasar kofin nahiyar Afirka ta bana, Ivory Coast, ta lashe gasar bayan ta ci Najeriya 2-1 a wasan karshe na AFCON
Masana tattalin arziki a Najeriya na ganin matakan da gwamnatin kasar ke dauka da kyar za su yi tasiri, idan dai ba an kawo karshen matsalar tsaro da kuma dawo da tallafin man fetur da bude iyakoki domin shigowa da abinci cikin kasar ba.
Zuwa yanzu hukumomi a Amurka da Najeriya, da kuma wasu masu fada a ji a Najeriya, sun tabbatar da mutuwar babban shugaban Bankin Access da iyalinsa.
Da alamar gwamnatin Najeriya ta fara daukar matakin rage matsalar rashin abinci da tsadarsa a fadin kasar biyo bayan korafe korafe da zanga zangar da aka yi a wasu sassan kasar kan tsadar rayuwa.
Tsadar rayuwa da hauhawar kayan masarufi, wani abu ne da ya addabi ƴan Najeriya, wanda kuma a tarihin kasar, ba'a taba fuskantar irin wannan kunci na rayuwa ba, wanda har yasa wasu gudanar da zanga-zanga.
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano, PCACC, tayi barazanar yin dirar mikiya akan manyan dakunan adana kayayyaki ko sito-sito da ake boye kayan abinci da nufin kara tsananta mawuyacin halin da al’umma suke ciki.
Gwamnan Na Neja, Muhammad Umar Bago ya sanya kwarya-kwaryan haramci akan sayarwa ko rarraba kayan abinci da sauran amfanin gona da aka noma a jihar zuwa sauran jihohin Najeriya.
Gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, a ranar Juma'a yace za a ladabtar da hukumomin da ke da hannu wajen yin damfara a kasuwar canji, bayan wani bincike da aka gudanar ya taimaka wajen dakile ta'addancin da ake yi na biyan kudade "ta daidaituwar lissafi."
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.