Ganin yadda talakawa su ka fara zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa a wasu yankunan Najeriya ya sa Majalissar Limamai da Malamai ta jihar Kaduna jawo hankalin gwamnati don kada a bar lamarin ya kazance.
Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya yi ta’aziyar rasuwar Asagba na Asaba, Mai Martaba Sarki, Obi Joseph Chike Edozien (CFR) wanda shine Asagba na 13 na garin Asaba dake Jihar Delta, ya kuma cika ne a ranar Laraba.
Wani matashi dan bautar kasa (NYSC), da wani jigon jam’iyyar APC, Cairo Ojuogboh da Mataimakin Ma’aji na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) Ayuba Abdullahi sun mutu sakamakon kallon wasan tawagar Najeriya ta Super Eagles da ta takwarkta ta Afirka Ta Kudu Bafana Bafana.
Kasa da makonni biyu da kasashen Nijar, Burkina Faso da Mali suka sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS mai kula da tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma a hukumance, kungiyar ta kira wani babban taro.
Masana sun bayyana cewa, jan ragama da akalar rayuwar talakan kasa ya ta’allaka ne a wuyan gwamnati ta kowani fanni kama daga samar da ilimi, lafiya, tsaro da kuma abun dogaro da kai.
Najeriya za ta kara da Kwaddebuwa a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairun da mu ke ciki bayan kasashen biyu su ka yi nasara a wasan kusa da karshe na gasar da suka fafata yau, Laraba, 7 ga watan Fabrairu.
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce ta kama wasu mata guda uku da ake zargin suna da hannu wajen shirya zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a jihar Neja a ranar Litanin din nan da ta gabata.
A cewar Mataimakn Shugaban Najeriyar kaddamar da jiragen na cikin kudurorin gwamnatin tarayya na yakar matsalar tsaron dake addabar kasar.
Ofishin Hulda da Kasashen Waje na Afirka ta Kudu (DIRCO) ya mayar wa Ofishin Jakadancin Najeriya martani kan wata sanarwa da ta fitar tana bawa 'yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu shawarar gudanar da bikin murna idan har Super Eagle tayi nasara akan Bafana-Bafana.
Dan shekara 12 daga jihar Nasarawa ya nuna matukar natsuwa da kuma mayar da hankali kan boko, inda ya zarce wasu 19 da suka fafata a babbar gasa ta karshe da aka gudanar a hedikwatar MTN da ke Ikoyi a Legas.
Kasashen biyu dama sun dade da jure hamayya ta tsawon shekara guda, saboda su ne ke da masana'antun nishaɗi mafiya girma a Afirka, kuma kusan su ne mafiya karfin tattalin arziki a nahiyar.
A yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan tsananin tsadar rayuwa a kasar, suma ‘yan jaridun kasar sun ce suna cikin yanayi na tsaka mai wuya musamman yadda aikinsu na kokarin ankarar da gwamnati halin da ‘yan kasar ke ciki da kuma hanyoyin shawo kan matsalolin da suke fuskanta.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.