Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ivory Coast Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirka Bayan Ta Ci Najeriya 2-1


Kofin gasar AFCON (AP)
Kofin gasar AFCON (AP)

Masaukin Bakin gasar kofin nahiyar Afirka ta bana, Ivory Coast, ta lashe gasar bayan ta ci Najeriya 2-1 a wasan karshe na AFCON

Najeriya ne ta fara zura kwallo bayan da mai tsaron baya, Williams Troost Ekong ya farke saura minti 7 kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Ama a minti 63, masaukin bakin suka rama, inda Franck Kessie ya zura wa Kwaddebuwa.

Najeriya ta canja dan wansan tsakiya nan Samuel Chuwkueze da Moses Simon a minti na 56 sannan Kwaddebuwa ta canja 'yan wasa biyu.

Stephane Singo ya karbi Serge Aurier sannan Max Gradel ya maye gurbin Oumar Diakite a baya da tsakiya.

Sai dai a miniti na 81 Sebastien Haller ya zura kwallo na biyu wa masaukin bakin.

Najeriya ta sake sauya 'yan wasantaa minti na 86, a yayin da Joe Aribo ya maye gurbin Zaidu Sanusi, Terem Moffi ma ya maye gurbin Frank Onyeka a karawar a minti na 86.

Kwaddebuwan ta yi nasara ne bayan an kara akalla minti 8 a wasan, inda aka tashi ci 2-1

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG