Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kalubalanci hukumar EFCC, mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, data kara kaimi a yakin da take yi da annobar damfara ta hanyar amfani da kafar sadarwa ta intanet da sauran nau'ukan almundahana.
Daraktan Cibiyar Samar da Bayanai a Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya ce suna sane da kalubalen tsaron da a halin yanzu ake fuskanta a sassa daban-daban na kasar.
Yayin da al'ummomin wasu yankunan Najeriya ke farin ciki a kan matakan da mahukunta suka dauka wadanda suke fatar su kawo sauki ga matsalar rashin tsaro, wasu kuwa fargaba ce ta karu gun su domin suna ganin barayin zasu kwararo yankuan su ne daga yankunan da aka dauki matakan.
Kungiyar kwadago ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya ma'aikata Naira dubu dari 4 a matsayin matsakancin albashi bisa la'akari da tsadar rayuwa.
Majalisar Dattawa ta sake gayyatar daukacin jami'an tsaron kasar a mako mai zuwa domin tattaunawa tare da samar da mafita kan matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar.
Wata gobara da ta tashi ta lalata shaguna da dama a babbar kasuwar Gusau, na jihar Zamfara a Najeriya, inda ta kashe mutum daya.
Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Ahmadu Fintiri a matsayin gwamnan jihar Adamawa inda mai shari’a John Okoro wanda ya shirya kuma ya karanta hukuncin a ranar Laraba ya yi watsi da karar da ‘yar takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Aisha Dahiru ta shigar.
Najeriya ta yi Allah Wadai da ficewar Jumhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso daga Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO duk da cewa ya zuwa yau Kungiyar ta ce ba ta samu wata sanarwar ficewar kasashen ba.
A ranar Litinin da daddare ne wasu ‘yan bindiga a Najeriya suka yi garkuwa da dalibai shida da malamai uku daga wata makaranta da ke kudu maso yammacin jihar Ekiti, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana a ranar Talata, a wani rahoton na sace yara ‘yan makaranta da aka yi a kasar na farko bana.
Najeriya ta ce hukumomin sojin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso wadanda ba zababbun al’umman kasar ba ne sun zalunci al’ummarsu yayin da su ka dauki matakin hadin gwiwa na ficewa daga kungiyar ECOWAS.
Wasu da ake zargin mayakan IS ne sun kashe mutane 22 a hari da suka kai a wani kauye da ke yammacin Jamhuriyar Nijar kusa da kan iyaka da Mali, kamar yadda wasu majiyoyi na cikin gida suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a ranar Litinin.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.