Kamen masu aikata badala a wasu sassa na birni da kewayen Kano da damkewa tare da gurfanar da matashiyar nan da ke kalaman batsa Murja Kunya a kotu, na daga cikin abubuwan da suka sabbaba wannan takaddama.
Kasa da kwana 2 da rufe layikan sadarwa al’ummar Najeriya na kokawa a kan yadda wannan matakin ke ci gaba da jawo musu asara kuma wasu masana ke cewa a cikin lallami ya kamata a bi yan kasa don hade layukansu da lambar shedar dan kasa, wasu kuma na ganin dole a Fifita ‘yancin ‘yan kasa a kan komai.
A ranar 1 ga watan Maris din shekarar 2024, Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Daurawa ya yi murabus daga mukaminsa kan kalaman na gwamna Abba Kabir Yusuf wadanda suka soki ayyukan da Hisbah ke yi.
Jose Peserio ya sanar da gama aikinsa na horar da 'yan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya bayan tawagar ta kai wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON a kasar Ivory Coast.
A safiyar yau Juma’a 1 ga watan Maris ne kwamandan Hisbah Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana ajiye aikinsa na shugaban hukumar a shafinsa na Facebook biyo bayan rashin samun goyon baya wajen gudanar da ayyukan kauda badala.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da zanga-zangar da kungiyar Najeriya NLC ta yi a fadin kasar domin nuna adawa da tsadar rayuwa da yunwa, inda ya gargadi kungiyar kwadago da ta sani cewa, ba ita kadai ce muryar jama’a ba.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya kaddamar da layin dogo 'Red line' na zamani a birnin Legas.
Shelkwatar rundunar sojin Najeriya da ke Jos, jihar Filato ta gurfanar da wasu jami'anta goma sha bakwai a gaban wata kotu ta musamman, bisa zarginsu da aikata laifukan da suka sabawa tsarin aikinsu.
Kungiyar kwallon kafa ta Chippa United ta wallafa a shafinta na X cewar, Nwabali na daga cikin ‘yan wasan da suka yi fice a gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) na shekarar 2023.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.