Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakan Da Gwamnatin Najeriya Ta Dauka Na Kayyade Farashi Ba Zai Kawar Da Yunwa Ba - Masana


Kayan abinci
Kayan abinci

Masana tattalin arziki a Najeriya na ganin matakan da gwamnatin kasar ke dauka da kyar za su yi tasiri, idan dai ba an kawo karshen matsalar tsaro da kuma dawo da tallafin man fetur da bude iyakoki domin shigowa da abinci cikin kasar ba.

‘Yan Najeriya, musanman talakawa na ci gaba da kukan tsada da hauhawar kayan masarufi a kasuwannin kasar.

Biyo bayan zanga zangar lumana da wasu mata suka jagoranta a jihar Neja da kuma wasu daban da aka gudanar a jihohin Kano da Osun, ya sa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, daukan matakan ba da umarnin fito da tan-tan na abinci da ke runbunan gwamnantin kasar, domin karya farashin kayan masarufi da ke neman ya gagari kundila.

To sai dai kuma a cewar wani masanin harkar gona, Farfesa Abubakar Gudigi, na jami’ar Ibrahim Babangida da ke Lapai a jihar Neja, ya ce da sake a wannan dabara ta gwamnati.

Gudigi ya ce matakin gwamnati na karya farashi, ba shi zai kawar da yunwa ba, domin yanzu haka akwai wadanda ke sayen kayan abinci a kauyuka, domin sayarwa da tsada, haka kuma dole a karya farashin kayan masarufi da dawo da darajar Naira.

Ko a makon da ya gabata sai da wata kotun tarayya da ke jihar Legas ta umarci gwamnatin Najeriya da ta dauki kwararan matakai na kawo karshen hauhawar kayan masrufi na kafa hukumar kaiyade farashin abinci ta kasa.

Wasu ‘yan Najeriya sun cewa akwai bukatar gwamnati ta dauki mataki na dawo da darajar Naira da bunkasa noma da tattalin arziki dama dawo da tallafin man fetur.

A bangarensa dai Farfesan harkar Noma Abubakar Gudigi cewa ya yi akwai matakin da gwamnati ya kamata ta dauka na hana manyan ‘yan kasuwa shiga kauyuka domin saye kayan gona daga manoma.

Yanzu dai a yayin da gwamnati ta dauki matakai na rage farashin kayan abinci, abun jira a gani shi ne ko matakan zasu taimaka wajen kawo sauki ga ‘yan kasa.

Saurari cikakken rahoton Babangida Jibrin:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG