Tsadar rayuwa da hauhawar kayan masarufi, wani abu ne da ya addabi ƴan Najeriya, wanda kuma a tarihin kasar, ba'a taba fuskantar irin wannan kunci na rayuwa ba, wanda har yasa wasu gudanar da zanga-zanga.
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano, PCACC, tayi barazanar yin dirar mikiya akan manyan dakunan adana kayayyaki ko sito-sito da ake boye kayan abinci da nufin kara tsananta mawuyacin halin da al’umma suke ciki.
Gwamnan Na Neja, Muhammad Umar Bago ya sanya kwarya-kwaryan haramci akan sayarwa ko rarraba kayan abinci da sauran amfanin gona da aka noma a jihar zuwa sauran jihohin Najeriya.
Gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, a ranar Juma'a yace za a ladabtar da hukumomin da ke da hannu wajen yin damfara a kasuwar canji, bayan wani bincike da aka gudanar ya taimaka wajen dakile ta'addancin da ake yi na biyan kudade "ta daidaituwar lissafi."
A cewar shugaban na Najeriya, za a rika karanta wannan alkawari na nuna biyayya ga kasa (National Pledge) a tarukan gwamnati da sauran taruka da jama’a suka shirya.
A ranar Laraba ne Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da fara daukar Ma’aikatan Kungiyar Likitoci ta kasa (NMT) zuwa aikin hajjin bana a kasar Saudiyya.
Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ne ya jagoranci tawagar ‘yan wasa na Najeriya yayin zaman nuna jimamin inda aka yi tsit na dan wani lokaci don yi wa mamatan addu’a.
Matsalar karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki da ake fama da ita a kasar hade da kunci rayuwa ya sa gwamnatin tarayya ta ba da umarnin sakin shinkafa da masara tan dubu 102,000 ga ‘yan Najeriya.
Majalisar Wakilan kasar ta bawa jama'a hakuri kan matsalar tsananin rayuwa da sha'anin tattalin arziki ya sa ake fama da ita, inda ta sha alwashin magance lamarin cikin gaggawa.
Ganin yadda talakawa su ka fara zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa a wasu yankunan Najeriya ya sa Majalissar Limamai da Malamai ta jihar Kaduna jawo hankalin gwamnati don kada a bar lamarin ya kazance.
Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya yi ta’aziyar rasuwar Asagba na Asaba, Mai Martaba Sarki, Obi Joseph Chike Edozien (CFR) wanda shine Asagba na 13 na garin Asaba dake Jihar Delta, ya kuma cika ne a ranar Laraba.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.