Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Bankin Access, Herbert Wigwe, Da Iyalinsa Sun Mutu a Hatsarin Jirgin Sama


Herbert Wigwe
Herbert Wigwe

Zuwa yanzu hukumomi a Amurka da Najeriya, da kuma wasu masu fada a ji a Najeriya, sun tabbatar da mutuwar babban shugaban Bankin Access da iyalinsa.

Babban Shugaban bankin Access Bank, Herbert Wigwe, da matarsa, da kuma wani dansa sun mutu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu daura da kan iyakar jahohin California da Nevada na Amurka. Jimlar mutane 6 ne ake kyautata zaton sun mutu a hatsarin na daren Jumma'a zuwa asubahin yau Asabar.

Dandalin yanar gizo na kafar labarai ta Fox News ya ce hatsarin ya auku ne a hamadar Mojave da ke jihar California da daren jiya Jumma’a bisa ga bayanan hukumomi.

Dandalin na Fox News ya ce hukumomin Najeriya sun tabbatar da mutuwar Wigne a kafar sada zumunta, ciki har da Daraktar Hukumar Cinakayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala.

Kafar labaran ta Fox News ta ce cikin wadanda su ka mutu din har da kuma tsohon Babban Chairman din Nigerian Exchange Group, kuma wai fitaccen dan siyasa a Najeriya, Mr Godwin Obaseki, ya tabbatar da mutuwar matar Wigne din da dansa.

Tuni dai kafafen yada labaran Najeriya su ka shiga yada wannan labarin, ciki har da jaridar nan ta Premium Times mai sauran yada labari.

- Fox News

-Premium Times

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG