Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsadar Rayuwa: A Najeriya Mazaje Na Gudu Su Na Barin Iyali


Kayan abinci na dada tsada a Najeriya
Kayan abinci na dada tsada a Najeriya

Bincike ya nuna cewa halin matsatsin rayuwa da yan Najeriya suka samu kansu cike ya dada ta’azzara a cikin watan Disamban shekarar bara, inda kudaden saye da gudanar da ayyukan yau da kullum suka haura kashi 28 da digo 92 cikin dari, wanda a da yana matakin kashi 28 da digo 20 ne cikin dari a watannin baya.

Har ila yau binciken ya gano cewa janye tallafin albarkatun man fetur ya janyo hauhawar farashin kayakin amfanin yau da kullum,
da su ka hada kayan abinci, muhalli, magunguna da suturar sawa da kuma zirga-zirga; sai uwa uba tabarbarewar darajar naira a kasuwanni.

A wani rahoto da hukumar kare yancin dan adam ta kasa shiyyar Gombe ta fitar ta hannun kakakinta, Mr.Ali Alola Alfinti, ta bayyana cewa saboda wannan matsatsi da magidanta su ka samu kansu ciki, ta samu korafe- korafe guda 280 a shekarar da ta gabata , inda ta tantance cewa daga cikin korafe korafe 280 an tabbatar cewa lallai magidanta 106 sun kaurace ma gidajensu sabili da kasa daukar dawainiyar iyalansu.

Kan wannan batu wakilinmu a Bauchi da Gombe ya tuntubi wani magidanci a garin Gombe, mai suna Garba Tela Herwa Gana Wudil Gombe, wanda kimanin shekaru hamsin kenan da yin aure,
ya na da yaya goma; ya bayyana min yadda halin da magidanta ke ciki, har da abubuwan da ya shaida da idonsa, na gudun magidanta da kuma yawon bara da ake ta yi har ma da yara kanana.

Kan wannan batu wakilinmu ya tuntubi Malam Abdullahi Yelwa, malami a sashen nazarin muggan dabi’u da dakile yaduwarsu a kwalejin Kimiyya da fasaha da ke Bauchi, wanda ya yi tsokaci kan wannan halin rayuwa, ya na mai bayyana hadarin da al’umma ke ciki sanadiyyar wannan al’amarin.

Shi ma Comrade, Aliyu Muhammed Wayas, Babban Jami’in Gamayyar Kungiyoyin kare hakkin dan adam shiyyar Arewa Maso Gabas, ya yi bayani tare da bayyana damuwa kan wannan al’amarin.

A gefe guda, a wani taron gangami agarin Lere da ke karamar Hukumar Tafawa Balewa, Gwamnan Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya yi bayanin halin kuncin da yan kasa ke ciki da kuma bayyana matakan da za a dauka, ya na mai kiran kowa ya bayar da gudunmowarsa a wannan al’amarin baya ga matakan da gwamnati za ta dauka.

Saurari rahoton Abdulwahab Muhammad:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG