Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsadar Abinci: Gwamnati Za Ta Fara Raba Kayan Abinci A Fadin Najeriya - Kwamiti


Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Da alamar gwamnatin Najeriya ta fara daukar matakin rage matsalar rashin abinci da tsadarsa a fadin kasar biyo bayan korafe korafe da zanga zangar da aka yi a wasu sassan kasar kan tsadar rayuwa.

Za a raba ton 42 na kayakin abinci iri iri wadanda za a fitar daga runbunan ajiye abincin baya ga shinkafa tirela 2000 da za a sayo daga wurin ‘yan kasuwa don rabawa ma jama’a. Wannan bayanin ya fito ne daga wurin kwamitin Ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa biyo bayan korafe korafen rashin abinci da kuma tsadarsa a fadin Najeriya.

Kwamitin ya yanke wannan shawarar ce bayan zaman da ya yi na kwanaki uku don tattaunawa kan hanyoyin da za a bullo ma matsalar karancin abinci da kuma tsadarsa a Najeriya.

Mamban kwamitin kuma Ministan Yada Labaran Najeriya, Alhaji Muhammad Idris, wanda bayan zaman kwamitin na uku ya yi karin bayani ma wakilin Muryar Amurka a Fadar Shugaban Najeriya, Umar Faruk Musa, ya ce

To amma Shugaban Kungiyar Manoma ta Najeriya, Alhaji Kabiru Ibrahim Faskari, ya ce ya kamata a hada irin wannan matakin da tsarin tallafa ma manoma da na’urorin zamani a farashi mai rahusa kuma ya zama tsari ne na dindindin ba sau daya kawai ba ko kuma idan ta dauro kawai ba. Ya ce kodayake gwamnati ba ta da isasshen kudin da za ta tallafa ma mutane da kayan abinci kyauta, ya kamata shi ma kayan abincin a sayar ma talakawa a farashi mai rahusa.

Minista Idris ya gargadi ‘yan kasuwa da ke sayen kayan abinci su kuma boye don su sayar daga baya da matukar tsada da su daina. Ya ce gwamnati ta san irin wadannan ‘yan kasuwa kuma idan ta kama za ta dau mataki a kan su.

Ya ce tunda bayarwa kyauta na iya janyo ribibi da rudami a wuraren raba abincin, sayarwa a farashi mai rahusa zai dan rage ribibi da hargowa. Ya kuma ce ya kamata gwamnati ta tabbatar wadanda ke matukar bukata aka fi bai wa fifiko wajen rabawa, ba magoya bayan jam’iyya ba. Kuma a tabbatar duk wanda aka ba shi abincin bai sayar ba.

Saurari rahoton Umar Faruk Musa:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG