Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu ya ce ba lalle sai an kafa kotuna na musamman ba don sauraron shari'un cin hanci da rashawa.
Bayan samun labarin ba wa Murjah Ibrahim Kunya beli, kafafen sadarwa ya cika da jita-jitar cewar Kwamandan Hisbah, Shiek Aminu Ibrahim Daurawa, ya ajiye aikinsa sakamakon ba da belin da kotu ta yi.
Shugabanni a gundumar Kufanan karamar hukumar Kajurun da 'yan bindiga su ka kai hari, sun ce kone mutane da rumbunan abinci da aka yi babbar barazana ce ga al-umar garin Gindin Dutse Makyalin.
Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo, ya yi kira ga shugabanni da gwamnatocin kasashen Afirka da su hada kai, su dau matakin zuba hannun jari na kashi talatin cikin dari a cibiyoyin hada-hadar kudi na Afirka da nufin inganta ma’aunin wadannan cibiyoyi yadda za su tallafawa ci gaban Afirka.
‘Yan Najeriya na fuskantar daya daga cikin yanayi mafi muni na tabarbarewar tattalin arziki a kasar ta Yammacin Afirka a cikin shekaru da dama sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.
NLC ta ce za ta shiga yajin aikin a ranakun 27 da 28 na wannan wata na Fabrairu don jan hankalin hukumomi kan yadda ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa.
Hukumar kare hakkin masu sayan kaya ta kasa (FCCPC), ta rufe katafaren kantin Sahad Store, a unguwar Garki dake birnin Abuja.
Farashin kaya a Najeriya na cigaba da tashi babu kakkautawa a farkon shekara nan, kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa NBS ta bayyana a rahoton da ta fitar.
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya umarci Mai Bashi Shawara Akan Harkokin Tsaro, Nuhu Ridadu da babban Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun da Darakta Janar Na Hukumar Tsaron Farin Kaya Ta Dss, Yusuf Bichi su hada kai da gwamnonin jihohi wajen farautar ‘yan kasuwar dake boye kayan abinci.
Gwamnatocin tarayya da na jihohin Najeriya 36 na nazari akan bukatar kafa rundunonin ‘yan sandan jihohi.
A yayın da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan tsananin rayuwa sakamakon tsadar abinci, magunguna da wasu ababen rayuwar yau da kullum, gwamnatin Najeriya ta bakın Ministan Noma, ta ce nan da mako mai zuwa, zata fara raba hatsi kyauta ga manoma musamman mabukata don rage matsalar yunwa a kasar.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.