Wasu yanbindiga sun hallaka mutane 3 tare da yin garkuwa da kimanin mutanen 30 a jihar Neja dake Arewa maso tsakiyar Najeriya.
Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin mutane 12 a matsayin mambobin Kwamitin kula da Manufofin Kudi na Babban Bankin Najeriya (CBN).
Duk da ganin zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa da wasu 'yan-Najeriya su ka fara, wasu shugabanni sun ce duk wani bore ba zai taimaki Najeriya ba.
Gwamnatin tarayya ta ce ta kammala shirye-shiryen farfado da shirin rabon kudade ga ‘yan Najeriya mafi talauci da bukata.
Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Janar Yakubu Gowon ya shawarci 'yan Najeriya cewa, kada yi saurin yanke hukunci kan ayyukan shugaba Bola Tinubu danganed a halin da kasar ke ciki.
Majalisar dokokin Kano ta yi karin haske dangane da mabanbantan wasikun da take karba daga kungiyoyi masu neman a sake fasalin dokar data kafa masarautun jihar guda biyar, sai dai masana na cewa, bada damar jefa kuri’ar raba gardama zai taimaka wajen waware wannan batu cikin ruwan sanyi.
Tsohon shugaban Najeriya kuma daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin nahiyar Afrika, Janar Yakubu Gowon, ya bukaci ECOWAS ta dage takunkumin da ta kakabawa kasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.
Shugaba Bola Tinubu ya nada Kemi Nanna Nandap a matsayin sabuwar Shugabar Hukumar Shige da fice ta Kasar Najeria.
Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) tayi kira ga kungiyar kwadago ta NLC, da ta jingine shirinta na gudanar da zanga-zanga domin ci gaba da wanzuwar zaman lafiya da walwalar jama’a.
Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta tsunduma cikin wani yajin aikin sai baba ta gani a jihar Neja, inda ta rufe ofisoshin gwamnati da asibitoci.
Kamfanonin simintin Najeriya sun amince su rage farashinsa zuwa tsakanin naira dubu 7 da dubu 8 akan buhu mai nauyin kilogiram 50 y danganta akan nisan wurin a fadin kasar.
Masana tattalin arziki sun ce ba 'yan canjin kasuwannin bayan fagge ke yi wa tattalin arzikin Najeriya gagarumar illa ba, wasu shugabannin bankunan kasuwancin kasar ne.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.