Najeriya ta amince da dawo da hasken wutar lantarki ga jamhuriyar Nijar bayan janye wasu takunkumai da Kungiyar Raya Tattalin Arziki Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, ta yi kan kasar.
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirta ta Yamma, ECOWAS, ta amince da ta dage wasu takunkumai da ta kakabawa kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.
Yayin da talakan Najeriya ke ci gaba da dandana kudarsa, hankula na dada karkata kan rawar da tashin farashin dala ke takawa.
Akeredolu ya rasu a kasar Jamus a ranar 27 ga watan Disambar bara bayan fama da rashin lafiya. Shekarunsa 67.
A cewar masanin, lokaci ya yi da matasa za su kara mayar da hankalinsu kan koyon ilimin na'ura mai kwakwalwa wanda hakan zai ba su dama su yi aiki daga ko'ina a duniya.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci babban bankin Najeriya CBN ya biya wani Bajamushe, Martin Gegenheimer Naira miliyan 63.7 da dala 10,000 bisa kama shi da tsare shi da hukumar kula da shige da fice ta Najeriya NIS ta yi ba bisa ka'ida ba.
Kamfanin Geometric Power Ltd na gab da bude sabuwar tashar wutar lantarki mai zaman kanta a garin Osisioma da ke yankin Aba na jihar Abia, wacce zata samar da megawatt 188 na wuta daga iskar gas, yayinda ake ci gaba da fuskantar matsalar karancin wutar lantarki a sassa daban daban na Najeriya,.
Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kashe Boderi Isyaku kasurgumin dan-fashin dajin nan da ya addabi jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara Naija da Abuja, tare da wasu manyan 'yan-bindigan dake tare da shi.
Ra'ayin masana ya banbanta dangane da wasikar da Tsohon Shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowan ya rubuta wa shugabannin ECOWAS, yayinda wadansu su ke gani ba za ta yi tasiri ba ganin cewa ya zo a kurarren lokaci, wasu kuma na ganin zata yi tasiri, la'akari da wadanda abin ya shafa.
Wasu yanbindiga sun hallaka mutane 3 tare da yin garkuwa da kimanin mutanen 30 a jihar Neja dake Arewa maso tsakiyar Najeriya.
Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin mutane 12 a matsayin mambobin Kwamitin kula da Manufofin Kudi na Babban Bankin Najeriya (CBN).
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.