Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu zai bar Abuja a gobe Alhamis zuwa birnin Addis Ababa na kasar Habasha domin halartar babban taron shugabannin kungiyar AU ta tarayyar kasashen Afirka.
Hukumomi a kasar Amurka sun fitar da hotunan wurin da mummunan hatsarin jirgin saman daya kashe Shugaban Rukunin Kamfanonin “Access Holdings” da wasu mutane biyar ya afku.
Gwamnatin tarayya ta bukaci hukumar ‘yan sandan kasa da kasa ta INTERPOL ta sanya idanu akan wasu ‘yan Najeriya uku akan zargin yin takardun bogi.
Biyo bayan kama fitattaciyar ‘yar Tiktok Murja Ibrahim Kunya da rundunar Hisbah ta jihar Kano ta yi, tuni suka mikata ga kotu domin hukuntata.
Kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a Afirka na fama da matsalolin tsaro da sosai da suka hada da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa a yankin arewa maso yammacin kasar, lamarin da ya kai makura.
Wasu ‘yan bindiga da a ke zargin ‘yan haramtacciyar kungiyar rajin Biafra ta IPOB ne, sun kai farmaki wata karamar ma’ajiyar daurarru da hukumomi su ka ce daurarru ne da ke gab da gama wa’adinsu, inda kuma harin ya yi sanadin tserewar wasu daurarrun, tare da kashe jami’in tsaro.
A daidai lokacin da duniya ke bikin ranar rediyo ta duniya, muna alfahari tare tayamu murnar gane irin gudunmowar da Sashen Hausa na Muryar Amurka yake bayarwa ga aikin jarida da kuma rawar da wakilanmu ke takawa wajen ilmantarwa da fadakar da al'ummar duniya.
Ana ci gaba da alhinin hadarin jirgin saman mai saukan angulu da ya yi sanadin salwantar rayukan mutane akalla shida ciki har da Shugaban bankin Access, Herbert Wigwe da matarsa da dansa.
Kamfanin kula da hannayen jarin rukunin kamfanonin “Access Holding” ya nada Bolaji Agbede a matsayin Shugaban Riko biyo bayan mutuwar Herbert Wigwe.
Biyo bayan kalubalen tsaro da ya dabaibaye yankin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriyua, rundunar ‘yan sandan birnin ta bullo da wani shirin samar da tsaro mai taken operation VELVET da a cikinsa ake fatan samun sauki.
A wani rahoton da ta fitar, asusun ba da lamuni ta duniya IMF, ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya na cikin wani mawuyacin hali, abinda ya sa farashin kaya a kasar ke hauhawa.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.