Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ribadu Ya Mayar Wa El-Rufa’i Da Martani Kan Gadar Tinubu


Nasiru el-Rufai (dama) da Nuhu Ribadu (Hagu)
Nasiru el-Rufai (dama) da Nuhu Ribadu (Hagu)

A martanin da ya mayar cikin wata sanarwa, Ribadu yace bai taba tattaunawa da kowa game da yin takara a 2031 ba.

Mashawarcin shugaban Najeriya a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bukaci al’umma su yi watsi da zarge-zargen da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya yi akansa.

A jiya Litinin El-Rufa’i ya zargi Ribadu da hannu a wahalhalun da ya sha a hannun hukumomin yaki da almundahana.

Yayi zargin cewar Ribadu na yin haka ne domin yana da burin gadar kujerar Shugaba Bola Tinubu a 2031.

A martanin da ya mayar cikin wata sanarwa, Ribadu yace bai taba tattaunawa da kowa game da yin takara a 2031 ba.

“Domin kawar da shakku, ina son in fayyace cewar ban taba tattaunwa da wani mahuluki game da yin takara a 2031 ba. Na sanya dukkanin karfi da tunanina wajen ciyar da Najeriya gaba tare da tabbatar da nasarar gwamnatin Shugaba Tinubu,” a cewar sa.

“Da ba don gudun kada a zaci shiru na a matsayin amincewa da zarge-zargen ba, da ba zan kula shi ba. Aikin da nake yi ya sha min kai da ba zai ba ni damar yin cacar baki a kafafen yada labaru da Nasiru el-Rufa’i ko wani mutum ba.

“Duk da yawan takala da hare-haren da yake yi ban taba fadin aibun Nasir a ko’ina ba. Na yi haka ne saboda mutunta alakarmu ta baya da kuma ta iyalanmu. Ba kuma zan fara hakan a yau ba.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG