Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattalin Arzikin Najeriya Ya Bunkasa Da Kaso 3.84 Cikin 100 A Zango Na 4 Na 2024 - NBS


Kayan abinci a kasuwar Najeriya
Kayan abinci a kasuwar Najeriya

Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kaso 3.84 cikin 100 a zango na 4 na shekarar 2024.

A cewar rahoton bunkasar tattalin arzikin da hukumar kididdigar Najeriya (NBS) ta fitar a yau Talata, bunkasar ta dara kaso 3.46 da aka samu a zango na 3 na 2024.

Alkaluman na yau Talata game da zango na 4 na shekarar 2024 sun kuma dara kaso 3.46 cikin 100 da aka bada rahoton samu a zagon na 4 na 2023.

Bangaren ayyuka ne ya mamaye galibin bunkasar ta zango na 4 na 2024, wanda ya karu da kaso 5.37 cikin 100 tare da bada gudunmowar kaso 57.38 cikin 100 na jumlar tattalin arzikin,” a cewar wani bangare na rahoton na NBS.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG