An rantsar da Lucky Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar Ondo, abinda ke alamanta farkon cikakken wa’adin mulkinsa na shekaru 4 bayan da ya maye gurbin gwamna Rotimi Akeredolu wanda ya mutu ya na kan karagar a shekarar 2023.
Bikin rantsarwar ya gudana ne a yau Litinin a filin wasa na jihar Ondo dake Akure, babban birnin jihar, watanni 2 bayan da ya lashe zaben gwamnan jihar karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Aiyedatiwa ya karbi rantsuwar kama aikinsa ne jim kadan bayan da aka rantsar da mataimakinsa
Daga nan sai gwamnan ya zagaya filin waya a cikin budaddiyar mota, yana jinjina ga magoya bayansa.
A ranar 17 ga watan Nuwamban 2024, hukumar zaben Najeriya ta ayyana Lucky Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ondo.
Bayan watanni ana yakin neman zabe, al’ummar jihar Ondo sun kamala zabe a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamban 2024, inda Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaben da kuri’u mafiya rinjaye.
Aiyedatiwa, gwamnan jihar mai ci ya samu kuri’u 366,781 inda ya doke abokin karawarsa na Jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Ajayi Agboola, wanda ya samu kuri’u 117,845.
Dandalin Mu Tattauna