Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar NNPP A Kano Sun Ki Amincewa Da Dakatarwa


Senator Suleiman Kawu NNPP Kano
Senator Suleiman Kawu NNPP Kano

A sanarwar hadin gwiwar da suka fitar, ‘yan majalisar tarayyar sun yi watsi da dakatarwar, inda suka bayyanata da wacce ta saba doka.

A jiya Litinin, reshen jihar Kano na jam’iyyar nnpp, ya sanarda dakatar da 4 daga cikin mambobinsa dake majalisun tarayya akan zargin sabawa muradan jam’iyyar.

Shugaban reshen Kano na jam’iyyar, Alhaji Hashimu Dungurawa, ne ya sanarda sunayen ‘yan majalisun tarayyar 4 da dakatarwar ta shafa da suka hada da Kawu Sumaila da Ali Madakin Ginin da Sani Rogo da kuma Kabiru Alhassan Rurum.

Sai dai a sanarwar hadin gwiwar da suka fitar, ‘yan majalisar tarayyar sun yi watsi da dakatarwar, inda suka bayyanata da wacce ta saba doka.

Don haka ‘yan majalisar tarayyar, suka bukaci al’umma da su yi watsi da “wannan dandalin karya da yaudarar yayin da muka jajirce wajen karfafa NNPP karkashin halastaccen shugabancinta tare da tabbatar da cewa jam’iyyar ta hidimtawa al’umma, ba wai bukatar Kwankwaso ta son zuciya da mukarrabansa ba.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG