Majalisar wakilan Najeriya ta ce hauhawar shaye-shayen miyagun kwayoyi da cin zarafin da ke faruwa a gidaje babbar barazana ce da ka iya durkusar da Najeriya idan masu ruwa da tsaki ba su hada karfi da karfe ba.
Shugaban majalisar wakilan, Dr. Abbas Tajuddeen wanda ya kaddamar da gangamin yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi da kuma cin zarafin da ke faruwa a gidaje a shiyyar Arewa maso Yamma, ya ce yanzu dukkanin masu ruwa da tsaki sun amince su dunkule don tunkarar wanda matsala baki daya.
Taron gangamin wayar da kai kan ta'ammali da miyagun kwayoyin da majalisar wakilai tare da hadin gwiwar hukumar wayar da kan jama'a ta kasa NOA su ka shirya dai ya maida hankali ne wajen fadar da kungiyoyi gudummawar da za su bayar wajen magance wannan matsala musamman a yankin Arewa maso Yamma.
Shugaban majalisar wakilan Najeriya, Dr. Abbas Tajuddeen ya ce wannan matsala ta ta'ammali da miyagun kwayoyi da kuma cin-zarafin da akan samu a gidaje na neman ta'azzara a wannan yanki idan ba a gaggauta daukar mataki ba.
Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, Birgediya-janar Mohammed Buba Marwa mai-ritaya, shi ya gabatar da makala kan hadarin miyagun kwayoyi ga cigaban kasa kuma akwai bukatar taron dangin magance wannan matsala baki daya.
Alh. Hamisu Abubakar Meyere, shine shugaban hukumar wayar da kan jama'a na shiyyar Arewa maso yamma kuma ya ce adadin masu ta'ammali da miyagun kwayoyi a yankin na bukatar a tashi tsaye.
Sarakuna da malaman addini da kungiyoyin mata da matasa da dama ne su ka halarci wannan taro kuma sun ce suna da gudummawa da za su bayar.
Ganin yadda shaye-shaye ke illata rayuwar matasa da mata ya sa shugaban majalisar wakilan Najeriya ya tabbatar da cewa yanzu duk shekara sai an shirya irin wannan taro don murkushe matsalar baki daya.
A saurari rahoton tare da Isah L. Ikara
Dandalin Mu Tattauna