Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna ketare (NIDCOM) da tauraron tawagar kwallon kafar Super Eagles Ahmad Musa sun bukaci a gudanar da bincike game da mutuwar dan wasa Abubakar Lawal wanda ake zargin ya fado daga wani gini ya mutu a kasar Uganda.
A jiya Litinin aka bada rahoton mutuwa Lawal wanda ‘yan sandan Uganda suka ce dan wasan haifaffen Sokoto ya mutu ne bayan daya fado daga benen wani kaafaren kanti.
Sa’o’i bayan faruwar lamarin mai ban takaici, shugabar hukumar nidcom, Abike Dabiri-Erewa ta bayyana cewar akwai “ababen zargi” game da mutuwar Lawal.
Wannan abin takaici ne kuma kamar akwai rashin gaskiya. Muna bukatar a gudanar da cikakken bincike. Kada ayi rufa-rufa ko kadan. Wannan abin bakin ciki ne! @ahmad musa718 da @nidcom_gov za su tabbatar kuma suna bukatar a gudanar da cikakken bincike a bayyane, Allah ya jikansa tare da baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.
Wannan abin takaici ne kuma kamar akwai rashin gaskiya. muna bukatar a gudanar da cikakken bincike. kada ayi rufa-rufa ko kadan. Wannan abin bakin ciki ne! kamar yadda ta wallafa a shafinta na X da maraicen yau Talata.
@nidcom_gov za ta tabbatar kuma tan a bukatar a gudanar da cikakken bincike a bayyane, Allah ya jikansa tare da baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.”
Dandalin Mu Tattauna