Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Lalata Haramtattun Wuraren Tace Danyen Mai 18 A Neja Delta


Bututun mai.
Bututun mai.

Barayin da ake zargi sun arce bayan da suka hangi dakarun.

Dakarun rundunar sojin Najeriya ta 6, da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaron kasar, sun lalata haramtattun wuraren tace danyen man fetur 18, tare da kama mutane 17 da ake zargin barayin mai ne, da lalata kwale-kwalen zamani 10 da kuma kwato lita 25, 000 albarkatun man fetur din da aka sata a fadin yankin Neja Delta.

A cikin wata sanarwa mai dauke sa hannun mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin, Laftanar Kanar Danjuma Jonah Danjuma, rundunar ta tabbatar da cewar dakarunta sun samu wannan nasara ce sakamakon jerin samamen data kaddamar daga ranar 17 zuwa 23 ga watan Febrairun da muke ciki.

A cewar sanarwar, dakarun sun samu gagarumar nasara a jihar Rivers, musamman ma a kewayen kilomita 45 da yankin Idama na karamar hukumar Akuku-Toru, inda suka lalata wasu haramtattun matatun mai 2 masu aiki tare da cafke kwale-kwalen katako 3 dauke da lita 9, 000 ta danyen man sata.

Sanarwar ta kara da cewar a mahadar Ogale dake kan babbar hanyar Eket zuwa Fatakwal, dakarun sun kwace wata babbar mota makare da fiye da lita 3, 000 ta danyen man sata.

Sanarwar ta cigaba da cewar a garin Okwuzi dake karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni, dakarun sun gano wata haramtacciyar ma’adanar man sata dauke da fiye da lita 2, 100 ta man dizil da aka tace ta barauniyar hanya adane a cikin buhunhuna.

Ta kuma bayyana cewar barayin da ake zargi sun arce bayan da suka hangi dakarun.

Saurari rahoton Abubakar Lamido Sakkwato:

Sojojin Najeriya Sun Lalata Haramtattun Wuraren Tace Danyen Mai 18
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG