Reshen jami’ar jihar Kaduna, na kungiyar malaman jami’o’in Najeriya (ASUU) ya jingine yajin aikin da ya fara kwanaki kadan da suka gabata.
A Talatar da ta gabata kungiyar ta tsunduma wani yajin aikin sai baba ta gani sakamakon rashin warware wasu batutuwa tsakaninta da hukumomin jami’ar da suka samo asali tun daga shekarun 2009 da 2017.
Sai dai, an janye yajin aikin a jiya Lahadi sakamakon shiga tsakanin da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani yayi.
A sanarwar daya fitar, shugaban kungiyar asuu reshen jami’ar jihar Kaduna, Dr. Peter Adamu, yace gwamnatin jihar ta nuna tausayi da dattaku wajen warware takaddamar ta hanyar gaggauta sakin kudade domin biyan kaso 60 cikin 100 na kudaden albashin da aka rike a watan Satumban 2017 dana kudaden alawus-alawus na kula da dalibai masu neman sanin makamar aiki na zangon karatu 5.
Dandalin Mu Tattauna