Jami’an rundunar shiyyar Maiduguri na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, ta kama su a ranar Talata, 5 ga wannan watan na Maris.
Rahotanni daga Ngala hedkwatar Gambarou Ngala a jihar Borno, na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da kimanin mutane 319.
Al ‘ummar yankin karamar hukumar Nafada a Jihar Gombe suna fuskantat wani yanayi mai tsoro da fargaba sakamakon bullar wata cuta da ta lakume rayukan yara da matasa sama da talatin.
Babban Kamfanin hada-hadar kudin crypto na Binance ya ce zai daina musayar kudin Najeriya na Naira daga ranar takwas ga wannan watan na Maris.
A wannan makon ne Najeriya ta fara shari'ar daruruwan mutanen da suka hada da jami’an hukumar zaben kasar da ake zargi da aikata laifukan da suka shafi babban zaben kasar na bara.
Mutum 11 ne suka sheka lahira, ciki akwai matuka 2 da wata mace.
A yayin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da kama wasu mutane 15 da ake zargi da wawure wani rumbun adana kayayyakin abinci a unguwar Karmo da ke Abuja, masana tattalin arziki da tsaro sun ce gwamnati ta san abun da ya kamata ta yi.
Ganin yadda matsalolin tsaro su ka ki ci, su ka ki cin yewa ya sa gwamnatin Najeriya shan alwashin sauya salo ta hanyar amfani da kimiyyar zamani wajen fuskantar 'yan-bindiga da sauran masu laifuffuka don magance matsar tsaro baki daya.
A yau Talata ne shugaban kwamandan Hisbah ta jihar Kano Mal Aminu Ibrahim Daurawa ya koma bakin aikinsa biyo bayan murubus da yayi a makon da ya gabata bayan wani jawabi da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yayi a gidan gwamnati yayin da yake ganawa da Malaman Addini.
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote na shirin kafa wata kungiyar hada-hadar man fetur, mai yiwuwa a birnin Landan.
Aliko Dangote, hamshakin dan kasuwa a Najeriya ya karrama marigayi Herbert Wigwe Shugaban Bankin Access, ta wajen sa sunan marigayin a kan hanyar shiga kamfanin man fetir na kamfanin Dangote.
Sheikh Aminu Daurawa ya dawo kan mukaminsa na Kwamandan Hukumar Hisbah, kwanaki kadan bayan yayi murabus.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.