Sheikh Aminu Daurawa ya dawo kan mukaminsa na Kwamandan Hukumar Hisbah, kwanaki kadan bayan yayi murabus.
Bankin Raya Kasashen Nahiyar Afrika (AFDB) ya sha alwashin tallafawa bangaren noman Najeriya da jarin dala milyan 134 da nufin bunkasa noman kayan abinci.
A jiya Lahadi ne, Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu da Sarkin Qatar, Mai Martaba Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani suka shaida bikin rattaba hannu akan wasu yarjeniyoyi masu tarihin gaske tsakanin kasashen 2.
'Yan kasuwar canjin kudi da dama sun nuna rashin gamsuwa da soke lasisin sama da kamfanonin canji 4000 da babban bankin Najeriya CBN ya yi.
A ci gaba da daukar mataki da dan adam ke yi kan sauyin yanayi da illolinsa, wata kungiya, da hadin gwiwar jihohin arewa maso yammacin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki, sun hadu a birnin kano, don neman mafita ta bai daya.
Jarumin barkwanci a masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood John Okafor, da aka fi sani da Mr. Ibu ya rasu.
Fitattaciyar ‘yar TikTok Murja Ibrahim Kunya ta shigar da kara gaban babbar kotun jihar Kano, bisa zargin keta mata haddi da rashin bin ka’idojin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar wajen shigar da karar da ake tuhumarta.
Babban Bankin Najeriya CBN ya soke lasisin wasu kamfanonin canjin kudi 4,173, cikin kimanin 5000 da ake da su.
Ba za a sami nasarar hade layikan salula da lambar Shaidar Dan Kasa ba idan ana amfani da karfin iko a maimakon bin mutane da lalama a cewar masana.
Kamen masu aikata badala a wasu sassa na birni da kewayen Kano da damkewa tare da gurfanar da matashiyar nan da ke kalaman batsa Murja Kunya a kotu, na daga cikin abubuwan da suka sabbaba wannan takaddama.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.