Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Ta Kama Wasu Manyan Motocin Kayan Abinci 21 Kan Hanyarsu Zuwa Kasashe Makwabta


Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja
Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja

Jami’an rundunar shiyyar Maiduguri na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, ta kama su a ranar Talata, 5 ga wannan watan na Maris.

WASHINGTON, D. C. - Sun kama manyan motoci 21 ne makare da kaya da kayan abinci da suka nufi N’djamena, Jamhuriyar Chadi, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Kamaru.

An kama motocin ne a wani samame da suka kai a manyan hanyoyin fita da ke kan titin Kalabiri/Gamboru Ngala da Bama a jihar Borno.

Bincike ya nuna cewa an boye kayan abinci da wayo a cikin manyan motocin da ba a gano su ba, amma ga yadda jami’an Hukumar suka sanya ido suka gano kayan abincin.

Wani bincike da aka yi ya nuna cewa shedar sayan kayayyakin da ke rufe a manyan motocin sun nuna za su je N’djamena, Jamhuriyar Chadi, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Kamaru ne.

Kamen da aka yi wa manyan motocin ana sa ran zai kawo karshen matsalar karancin abinci da marasa kishin kasa ke sa mutane fuskanta da kuma masu fasa kwauri a fadin kasar.

Ana kan binciken wadanda aka kama tare da manyan motocin kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG