Malamin Addinin Kiristan nan na Najeriya Bishop Mathew Kuka ya caccaki tsarin yadda ake rabon kayan tallafi ga 'yan Najeriya a daidai lokacin da halin matsin rayuwa ke kara ta'azzara a kasar.
Shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja ranar Talata zuwa Dakar, Senegal, domin halartar bikin rantsar da sabon zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye.
'Yan fansho a jihar Kano sun bukaci hukumar kula da asusun fansho ta jihar ta hanzarta sayar da gidajen da hukumar EFCC ta karbo musu, wadanda gwamnatin jihar ke rike da su fiye da shekaru goma da suka gabata.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da sakin Naira biliyan 25 ga Hukumar Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA) da Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasar (NHIA) domin fadadawa tare da inganta harkokin kiwon lafiya ga 'yan Najeriya.
A jihar Kebbi da ke Najeriya, wani lamari ya afku inda ake zargin wani soja ya harbe wani mutum har lahira saboda sace kayan abinci. A cewar wata majiya a jihar, an tura sojoji ne domin hana sace-sacen a wani wurin da aka ce mazauna yankin na kwashe kayan abinci.
Domin murnar zagayowar ranar Ista, Tinubu a cikin sanarwar daya fitar a yau Juma'a, ya bukaci Kiristoci su rungumi halayen kauna da sadaukarwa da tausayin juna da ake dangantawa da wannan lokaci.
A yau, ranar da ake kira 'Good Friday', wato Jumma'a mai kyau, rana ce da mabiya addinin Kirista ke imanin an giciye Yesu Kristi, kamar yadda Allah ya tsara, domin ya kasance mai ceton dukkan bil'adam, daga shiga jahannama.
Kasa da sa’a 24 bayan fitar da sanarwar da hedkwatar tsaron Najeriya ta yi, basaraken, Clement Ikolo ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar Delta inda ya ce ba shi da hannu a kisan sojojin.
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna yayi tayin bada ilmi kyauta ga daliban makarantar Kuriga da aka kubutar a karkashin gidauniyarsa.
A ranar Alhamis ne Shelkwatar Tsaron Najeriya ta bayyana cewar, Babbar Kotun Tarayya dake Borno ta bada umarnin sakin akalla mutane 313 da sojoji suka kana a bisa zarginsu da aikata laifin ta'addanci.
A daidai lokacin da wasu ‘yan Najeriya ke korafe-korafe a kan kayyade yawan kudin da zasu rika cira a ATM ko kuma a cikin banki da ake kallo a matsayin yiwuwa akwai karancin takardun kudi ne a kasar, masu ruwa da tsaki a fannin hada-hadar kudi a bankuna sun ce babu matsalar karancin kudi.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.