Wata babbar kotu da take Kano a Najeriya ta yankewa ‘dan China Frank Geng-Quangrong da ya kashe Ummulkhulsu Buhari har lahira a shekara 2022 hukuncin kisa ta hanyar rataya
Mawallafin Desert Heral da ke Kaduna, Tukur Mohammed Mamu, ya yi barazanar maka babban lauyan gwamnatin tarayyar Najeriya kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), a kotu saboda ayyana shi a jerin masu daukan nauyin ta’addanci a kasar.
Dalibai shida na makarantar Kuriga da aka kubutar daga hannun masu garkuwa da mutane suna jinya a Kaduna, kamar yadda rundunar sojin ta bayyana a jiya.
Babban hafsan tsaron Najeriya Janar Chris Musa ya ce masu ba da bayannan sirri ga sojojin ke kawo cikas ga yaki da kungiyoyin masu garkuwa da mutane da ke ci gaba da sace dalibai da mazauna arewacin kasar.
Gwamnan ya dage kan cewa dalibai 137 da malami daya 'yan-bindigan suka sace kuma gaba daya daliban sun dawao sai dai malaminsu ya rasu a hannun 'yan-bindigan tun a daji.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta IHRC-International Human Rights Commission ta shiga jerin masu bukatar majalisa ta sauya matsaya kan dakatar da Sanata Abdul Ningi.
Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ya tabbatar da tserewar manajan yankin Binance na Afirka, Nadeem Anjarwalla daga Najeriya.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dauki matakin shari'a akan binance, wani fitaccen dandalin hada-hadar kudin kirifto
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta baiwa gwamnatin jihar Kano tallafin tireloli 100 na shinkafa, tirelolin dawa 44 da na masara guda hudu domin rabawa ga mabukata.
A kalla mata hudu ne suka mutu yayin da daya ta jikkata sakamakon turmutsitsin da ya barke yayin da jama’a suka taru domin karbar tallafin kudade a arewacin Najeriya a ranar Lahadi, kamar yadda ‘yan sanda suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Tashin hankali tsakanin al'ummomin Hausawa da Fulani a Najeriya na ci gaba da kawo cikas ga kokarin samar da zaman lafiya musamman a yankunan arewacin kasar.
Bisa yanda canjin dala ke hawa da sauka, hukumar alhazan Najeriya ta ce duk wanda zai biya kujera yanzu zai bada daga Naira 8, 254, 464 a arewa sai Naira miliyan 8, 454, 464 a kudu.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.