Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Shugaban Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ya Koma Kan Aikinsa


Yadda Sheikh Aminu Daurawa Ya Dawo Kan Mukaminsa Na Shugaban Hukumar Hisbah
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00

Yadda Sheikh Aminu Daurawa Ya Dawo Kan Mukaminsa Na Shugaban Hukumar Hisbah

A yau Talata ne shugaban kwamandan Hisbah ta jihar Kano Mal Aminu Ibrahim Daurawa ya koma bakin aikinsa biyo bayan murubus da yayi a makon da ya gabata bayan wani jawabi da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yayi a gidan gwamnati yayin da yake ganawa da Malaman Addini.

KANO, NIGERIA - Jawabin dai na gwamna ya sa gwiwar kwamandan na Hisbah yayi sanyi kamar yadda ya fada a shafinsa na facebook a yayin da ya sanar da murabus dinsa daga shugabancin hukumar ta Hisbah.

Sheikh Daurawa (Hoto: Facebook/Hisbah)
Sheikh Daurawa (Hoto: Facebook/Hisbah)

Malamai da masu fada a ji ne na Arewacin Najeriya suka sanya baki domin tabbatar da cewa Malam Aminu Daurawa ya koma bakin aikinsa inda a daren jiya bayan ganawa da gwamna da kwamandan Hisbah ya bayyana dawowarsa kan aiki.

Ma’aikatan hukumar ta Hisbah da wasu jami’an gwamantin ne suka yi dafifi a ofishin na Hisbah domin tarbar kwamandan na Hisbah.

Taron Hisbah
Taron Hisbah

Yayi jawabi ga manema labarai , inda ya bukaci matasa da yan Tiktok masu gurbata tarbiyya da su sauya hali tare da basu makwanni biyu domin gyara halayyarsu ko kuma su fuskanci fushin hukumar.

Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Yadda Shugaban Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ya Koma Kan Aikinsa.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG