Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sheikh Aminu Daurawa Ya Dawo Kan Mukaminsa Na Kwamandan Hukumar Hisbah


Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sheikh Aminu Daurawa a fadar gwamnatin jihar Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sheikh Aminu Daurawa a fadar gwamnatin jihar Kano

Sheikh Aminu Daurawa ya dawo kan mukaminsa na Kwamandan Hukumar Hisbah, kwanaki kadan bayan yayi murabus.

KANO, NAJERIYA - Hakan ya biyo bayan ganawa da yayi da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin jihar Kano

An tattauna akan batutuwa masu muhimammnci na cigaban Kano da addinin Musulunci kuma kowanne bangare ya amince Mal Aminu Daurawa ya cigaba da shugabanci Hukumar ta Hisbah.

Ganawan ya biyo bayan yunkurin samar da maslaha ne dangane da kalaman da gwamna ya yi yayin wani taro da limaman Kano a ranar Alhamis, inda ya soki yadda hukumar ta Hisbah take gudanar da ayyukanta, wanda ya yi sanadin yin murabus daga ofishin kwamandan Hukumar Hisbah da Sheikh Daurawa yayı a makon da ya gabata.

A ranar 1 ga watan Maris din shekarar 2024 ne Sheikh Daurawa ya yi murabus daga mukaminsa.

"Mun yi iya kokarinmu, mu ga cewa muna abin da ya kamata, to amma ina ba mai girma gwamna hakuri bisa fushi da ya yi da maganganun da ya fada.

Ya kara da cewa, "kuma ina rokon a ya min afuwa, na sauka daga wannan mukami da ya ba ni na Hisbah..... inda muka yi kuskure muna fata a yafe mana." In ji Daurawa.

Kusan shekaru 22 da suka gabata aka kafa hukumar ta Hisbah a Kano don yin umarni da kyawawa da hani da munanan ayyuka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG