Wata kotun birnin Yamai ta umurci hukumomin jamhuriyar Nijar su gaggauta sakin wasu makusantan hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum daga inda ake tsare da su.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar hukumomin tsaro zasu fara farautar mutanen dake rike da takardun kammala karatun digiri na bogi a fadin Najeriya.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rattaba hannu akan kudirin dokar rancen dalibai, inda ya tanadi hukuncin zaman gidan gyaran hali ga duk wanda ya kasa biyan bashin.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yiwa ajin "A" na masu amfani da lantarki karin kudin wuta ajin "A" shine na masu samun lantarki tsawon sa"i'o 20 a rana.
Gwamnatin Zamfara ta bada umarnin gaggauta takaita zirga-zirga akan iyakar jihar da jihohin Sokoto da Katsina tun daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safiya saboda karuwar hare-haren 'yan bindiga akan matafiya.
An gudanar da jana'izan Dr Kamal Abdulkadir na jami'ar Maiduguri, malami a bangaren ilimin jiki da lafiya da aka yi wa kisan gilla.
Masu kamfanonin shirya tafiye-tafiye na ta bayyana yakinin cewa akwai yiyuwar farashin tikitin kamfanin airpeace ya yi tasirin kawo sauki a saura kamfanonin tafiye-tafiyen kasashen waje da suke takurawa ‘yan kasar nan da muguwar tsada bada jimawa.
A ranar Talata ce matatar man Dangote ta Najeriya ta fara samar da albarkatun man fetur ga kasuwannin cikin gida, in ji wani babban jami’in kamfanin da kungiyoyin sayar da man fetur, wani muhimmin mataki a yunkurin da kasar ke yi na samun dogaro kai a fannin makamashi.
Masu ibada a wani masallaci da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, sun tsere a ranar Talata a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka far wa mazauna yankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ne ya tabbatar da hakan ga gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Delta ta tabbatar da ceto dalibai 9 da aka sace a jihar.
'Ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa bisa yadda kayayyakin masarufi ke ci gaba da tashi a kasuwannin kasar, duk da cewa darajar Naira sai kara samun tagomashi yake yi.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.