Majalisar Dattawan Najeriya karkashin jagorancin Shugabanta, Godswill Akpabio, ta dakatar da Sanata Abdul Ningi a bisa zarge-zargen yin cushen naira tiriliyan N3.7 a cikin kasafin kudin bana.
Mambobin kungiyar NUEE sun kasa sun tsare a gaban babban ofishin hukumar raba wutar lantarki ta jihar Kaduna.
A yau Talata, wani ibtila'i ya abkawa jihar Borno, inda gobara ta kone sansanin 'yan gudun hijra na Muna dake shiyar Muna na jihar dake yankin arewa maso gabashin Najeriya, wanda yayi sanadiyar mutuwar yara 2.
A ranar Litinin din da ta gabata ne sojojin Najeriya suka fara farautar wasu masu garkuwa da mutane da suka yi awon gaba da daliban makaranta kusan 300 a jihar Kaduna kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana, yayin da iyayen dake cikin rudani suka bukaci a sanar da su lokacin sake haduwa da yaransu
Sojojin Najeriya sun fita farautar ‘yan bindigar da suka yi awon gaba da daliban makaranta kusan 300 a jihar Kaduna a makon da ya gabata, kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana, yayin da iyayen da ke cikin rudani ke bibiyar lokacin da za su sake sa ido ga 'ya'yansu.
Kungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'in Najeriya (SSANU) da takwararta ta Ma'aikatan Jami'ar da ba Malamai Ba (NASU) sun ayyana shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 7 tun daga ranar 18 ga watan Maris din da muke ciki.
A daidai lokacin da aka fara azumin watan Ramadan, Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya jaddada aniyar rundunar na samar da ingantaccen tsaro ga kowa a fadin Najeriya.
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin watan azumin Ramadan a Najeriya.
Yayin da al'ummar Musulmi a fadin duniya ke harmar fara azumtar wata mai tsarki na Ramadan, a Najeriya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya ce a fara duban wata daga yau.
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace wasu daliban makarantar allo ta almajirao a wani kauye da ake kira Gidan Bakuso a jihar Sokoto da ke Najeriya.
Asusun Tallafawa Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) yayi Allawadai da harin baya-bayan nan da aka kai kan wata makaranta a jihar kaduna.
Shugaban Kasar Najeriya, Bola Tinubu, ya sha alwashin cewar gwamnatinsa zata bada fifiko kan walwalar mata da kiyaye hakkokinsu tare da bunkasa rayuwarsu.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.