Rundunar Sojin Najeriya ta sha alwashin kubutar da fiye da yara 'yan makaranta 200 da 'yan bindiga suka sace a baya-bayan nan a jihar Kaduna.
Wata mata Esther Joseph ta ce ta yi “kusan hauka” don bacin rai lokacin da aka yi garkuwa da ‘yarta Precious Sim ‘yar shekara 13 daga makarantar sakandaren Arewacin Najeriya tare da wasu dalibai a ranar 5 ga Yuli, 2021.
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama mutane 11 da suka hada da mata daya da maza goma saboda laifin cin abinci da rana tsaka a bainar jama’a cikin watan Ramadan a jihar.
Wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da dalibai da ma’aikata 286 a wata makaranta a arewacin Najeriya a makon da ya gabata, sun bukaci jimillar Naira biliyan 1, kwatankwacin dalar Amurka 620,432 domin a sako su.
Dakarun rundunar hadin gwiwa ta aikin wanzar da zaman lafiya na "Operation Hadarin Daji" sun kubutar da mutane 10 da aka yi garkuwa dasu a garin Tsafe, shelkwatar karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, sakamakon tarwatsa maboyar 'yan bindiga da suka yi.
Kungiyoyinn Fulani makiyaya sun yi gagarumin taron neman bakin zaren dawo da martabar su a idon duniya daga kashin kajin da wasu ke shafawa mu su.
An samu barkewar hayaniya a yau Laraba biyo bayan rufe shahararriyar kasuwar Wuse a Abuja da hukumar gudanarwarta tayi sakamakon tashin gobara a cikinta a jiya Talata.
Najeriya ta samo tallafin dala biliyan 1.3 domin kammala aikin layin dogo da zai hada Kano, birni mafi girma a arewacin Najeriya zuwa Maradi dake makwabciyar kasar Nijar, in ji ma'aikatar sufuri a ranar Laraba.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bada umarnin gaggauta bude kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar. Haka kuma, ya umarci a janye dukkanin takunkuman da aka kakabawa kasar nan take.
Wasu ‘yan bindiga a Najeriya sun yi garkuwa da mutane 61 daga wani kauye da ke arewacin jihar Kaduna, kwanaki bayan da wasu ‘yan bindiga suka sace dalibai 300, kamar yadda mazauna garin suka bayyana a ranar Talata.
Sanata Abdul Ningi dai dan Jam'iyyar PDP ne kuma shi ne Shugaban Kwamitin kula da Yawan Jama'a wato National Population Committee sannan kuma Shugaban Kungiyar Sanatocin Arewa a Majalisar Dattawan.
Yadda kungiyoyin 'yan bindiga ke samun garkuwa da mata da yara a sauwwake, musamman a arewacin Najeriya, na kara ta'zzara da kuma tayar da hankali.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.