Hukumar Kwastan reshen tashan jiragen ruwa ta Tin Can ta kama wasu tarin makamai da kayan soji da alburusai da kuma muggan kwayoyi da aka yi yunkurin shigowa dasu Najeriya ta hanyan sumogal.
Sakamakon yawaitar matsalar satar mutane a Najeriya, gwamnonin arewacin kasar sun amince da yin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya da kuma duba yiyuwar yin amfani da wasu hanyoyin na daban wajen shawo kan karuwar matsalar tabarbarewar tsaro da take addabar yankin arewa.
Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana cewar matatar mai ta Fatakwal zata koma bakin aiki a watan Afrilu mai zuwa.
Hukumar NCC mai kula da harkokin sadarwa a Najeriya tace kamfanonin sadarwa na kokarin dawo da sadarwar intanet bayan data katse a jiya Alhamis.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnati ba za ta biya kudin fansa ba.
Atiku ya yi kiran ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya ce yin rufa-rufa kan lamarin da kuma dakatar da wanda ya kwarmata zancen ba mafita ba ce.
Wani mai sana’ar POS a Unguwar Kurnar Asabe da ke Jihar Kano ya mayar da kusan naira miliyan 10 da wani kwastomansa ya yi kuskuren tura masa a maimakon dubu 10.
Matasan Arewa da wata kungiyar kare 'yancin fararen hula da dimokradiya CISLAC, sun nuna cewa dakatar da Sanata Abdul Ningi a Majalisar Dattawa, dakile 'yancin fadin albarkacin baki ne.
Rundunar Sojin Najeriya ta sha alwashin kubutar da fiye da yara 'yan makaranta 200 da 'yan bindiga suka sace a baya-bayan nan a jihar Kaduna.
Wata mata Esther Joseph ta ce ta yi “kusan hauka” don bacin rai lokacin da aka yi garkuwa da ‘yarta Precious Sim ‘yar shekara 13 daga makarantar sakandaren Arewacin Najeriya tare da wasu dalibai a ranar 5 ga Yuli, 2021.
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama mutane 11 da suka hada da mata daya da maza goma saboda laifin cin abinci da rana tsaka a bainar jama’a cikin watan Ramadan a jihar.
Wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da dalibai da ma’aikata 286 a wata makaranta a arewacin Najeriya a makon da ya gabata, sun bukaci jimillar Naira biliyan 1, kwatankwacin dalar Amurka 620,432 domin a sako su.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.